*πŸ’ŸπŸ’Ÿ UWA KO ÝAπŸ’ŸπŸ’Ÿ*

*written by:*
*FAREEDAH GURKUπŸ’š*


*Edited by:ANEELURV😍*


*Dedicated to my lovely mom😍*


*pg 15▶16*



Kira ya tayar da feenerh da daddare ,tamanta batasa wayar a silent ba.
"Hello", ta faďi muryarta a ciki,
"Hello *D*",
Nan da nan idon feenerh ya kwashe,
"Dear",
"Naam *D*, yakike*",
"Lafiya kalau , dear kun kai lafiya",
"Kalau *D*, kwana biyu ban kira ba saboda ban siya sabon sim bane, abubuwa sun min yawa",
"Bakomai dear, nayi missing  Δinka sosai",
"Nima haka *D*, shiyasa nafara launching sim  Δina da numban ki",
"Owww thanks dear",
"Toh *D* nasan bacci kikeyi ,gobe zan kira ki saboda muyi hira sosai",
"Toh shikenan dear, gud night i love you ,sweet dreams",
Feenerh ta kashe wayar tana murnushi ,atlast musa ya kirata yanzu zata samu kwanciyar hankali, she can't wait gobe yayi saboda su kara yin magana. Anan tayi bacci da wayar a manne da kirjinta .
"Feenerh!!!"
Feenerh ta bude ido da kyar sai taga mamanta a tsaye ,
"Oh mommy gud morning",
"Kema haka, wato daga sallar asuba sai kika koma bacci koh, saboda yanzu ba makaranta",
"Wallahi mommy bahaka bane, nagaji ne sosai shiyasa",
"Wani aiki kika yi har kika gaji",
Feenerh tayi shiru ,batason mommy tasan jiya tayi night call da musa",
"Mommy nayi karatu ne jiya shiyasa kinsan mun kusa dawowa school",
"Lallai toh kitashi saboda yau daddynki yace yana son magana dake kafin ya tafi wurin aiki",
"Allah mommy, toh gani nan zuwa yan zunan".
Feenerh ta sami daddynta a zaune a falo ya gama shirin zuwa gurin aiki ,
"Daddy ina kwana",
"Lafiya kalau safiya, antashi lafiya",
"Lafiya kalau daddy",
"Toh safiya, abinda yasa na aika mamanki ta kira shine akan maganan da kukayi da ita ,kin tuna",
"Eh na tuna daddy",
"Toh yawwa ,wani decision kika dauka akai",
"Daddy naji abinda kuka ce kuma na gamsu da dakkan kalamominku ,nan da shekara daya in sha allah zan fito da miji kamar yadda kuka kayyatamun",
"Yawwa safiya,Γ½ar albarka kinga inkika yi hakan shi zai fiye miki saboda kowace mace gidan mijinta shine aljannarta",
"Toh daddy",
"Shikenan zaki iya tafiya yanzu",
"Toh daddy nagode".
Feenerh ta koma dakinta ,ta zauna shiru yanzu dai iyayenta da gaske suke son auran da ita ,kodai sun gaji da ita ne amma ai ita kaďai suke da ,baya yadda za'ace sun gaji da ita. Toh maybe shiya fiye mata alkhairi tunda ance abinda babba ya hango ,yaro koya hau saman tsauni baxai gani ba.
Kirar wayarta ne ya katse mata tunaninta tana dubawa sai taga kawarta ne khadija ,
"Hello khadija",
"Naam feenerh yakike",
"Kalau kalau babe ,ya hutu",
"Lallai muna nan muna shan hutu , ni duk na kosa ma mu koma",
"Nima haka kawata",
"Toh yanzu dai kina gida ne ",
"Eh ina nan",
"Toh gani nan zuwa ,i hope dai kin ajemana gist",
"Akwai gist kam sosai kawata",
"Toh gani nan zuwa",
"Sai kin shigo".




*tnx for reading....*
*©Fareedah*

Comments

Popular Posts