*πŸ’ŸπŸ’Ÿ UWA KO ÝAπŸ’ŸπŸ’Ÿ*

*written by :*
*FAREEDAH GURKU*

*Edited by :ANEELURV😍*


*Dedicated to my lovely mom😍*



*pg 21▶23*



Tafiyar musa yasa feenerh ta gano mahimmacin sa a rayuwarta ,he have made alot of changes to her life,yanzu ma ta tabbata cewa tana sonsa sosai ,kuma shi ya cancanci yazama mijin auranta in sha allah.
********************
Yau ja'afar zai dawo daga uganda kamar yadda khadija ta faďa.
Ja'afar wanda shine school father  Δinta ,tana respecting  Δinsa sosai sannan kuma tana murnar kammala karatunsa dayayi, kamar da wasa lokacin da yazo sallamarta zuwa uganda ,gashi har zai dawo.
Tasa laraba ta dafa masa favorite food  Δinsa wato garnished spaghetti saboda tasan anan zaiyi dinner.
Bayan tagama shirya kayan abincin a table sai ta shiga ciki don yin alwala tayi sallah. Tana zaune akan sallaya bayan ta idar da sallah sai text ya shigo,
"Dota gani a zaune a falo", da gudu tafito falo sai taga ja'afar a zaune a three seater,she can't believe it gaba daya ya canza kamar ba ja'afar da tasani ba, ta karaso ta zauna kusa dashi,
"Dad ,is it really you",
"Tabbas nine dota ,yakike",
"Lafiya kalau dad ,nayi missing  Δinka sosai",
"Nima nayi missing  Δinki dota",
"Kamar da gaske ,bayan nasan katafi wurin khadija kafin ka branching nan",
"For sure dota ,kinsan saina dubata saboda banson ta tsume batare data ganni ba"
Feenerh tayi dariya ,
"Ta tsume kuma dad",
"Eh mana",
"Toh dad ya hanya ,ya karatu, ya hutu",
"Duk lafiya",
"Dad....." ,bata karasa magana ba taji ance ,
"Ohhh wato kinada wani dad bayan niko safiya",
Ta juya taga ai daddynta ne ya dawo daga masallaci,
"No daddy, kasan kaine number one and the best",
Daddy ya danyi dariya sannan yace,
"Ja'afar Γ½en makaranta ,sannu da dawowa",
Ja'afar ya tsunguna ,"yawwa abba ,mun sameku lafiya",
"Lafiya kalau, har kun gama kenan",
"Eh abba",
"Lallai abin ba wuya ,kazo ganin kanwar nake ko",
"Eh ",
"Toh nina shige ta ciki",
"Toh sai anjima abba",
"Yawwa",
Daddy ya wuce, ja'afar ya koma ya zauna",
"Dama abba na nan",
"Eh yana nan ,yau ya dawo daga business trip  Δin",
"Okay ,dama mun riga munyi gaisuwa da umma",
"Toh dad muje ta dining kaci abinci ,laraba prepared your favorite",
"Allah ko,toh muje",
Sun isa dining table,taja masa kujera ya zauna sannan ta dauko plate tafara serving  Δinshi,ta zubo masa ruwa mai sanyi a glass  Δaya sannan tasa masa lemon kwakwa awani glass  Δin saita ta zauna tana kallonsa yana cin abinci.
Sai ya tuno mata da musa ,hankalinta ya daga amma ba ta nuna mai saboda har yanzu bata bashi labarin musa ba kuma tasanshi da bincike kamar CID.
Bayan ja'afar ya gama cin abinci sai yama feenerh godiya sannan yace zai tafi masallaci yayi sallar isha.
Itama tashiga ciki donyin sallar, bayan sallar isha ,ja'afar yashigo sannan yama feenerh waya ya sanar da ita cewa ya shigo.
"Sannu da dawowa dad", feenerh tace bayan tashiga falon.
"Yawwa dota",
"Dad yanzu tunda ka dawo, yaushe za'afara maganar aurenku da khadija",
"Very soon ,da zarar na gama services  Δina",
"Okay",
"Feenerh",
"Naam",
Feenerh ta amsa a tsanyaye ,saboda tasan da matsala tunda ja'afar yakirata da sunanta.



*tnx for reading....*
*©Fareedah*

Comments

Popular Posts