Al-hubh❤
Chapter one
Story by :Faridat gurku
Written by :Faridat gurku
Follow me at wattpad @phareadah
Bismillahi rahmanir rahim
Kaduna 1998
Yadda ahlin alhaji sani suka ga dare haka suka ga tsafe cikin tashin hankali, matarsa sadiya ke nakuda tun da daddare har tsafe a asbiti, likitoci na ta yin iya kokarin su amma abin ya kasa.
Daga karshe dai suka ce sai dai a shige da ita theatre, alhaji sani ya bada izinin a yi haka, kafin a wuce da ita sai wani nakuda mai bala'in zafi ya kamata kafin a ce me sai kukan baby ya mamaye ko ina.
Gaskiya yayi murna sosai saboda ba son aikin yakeyi ba, kuma yasan matar tasa ta wahala, gani yake kamar in tashiga theatre bazata rayu ba, ya amince ne kawai saboda likitocin suka umarce ayi hakan.

Koda ya tunkari babban likitan sai murmushi ya kwace masa,
'Nagode sosai likita, Allah ya sakamuku', ya faďi cikin nishadi da walwala.
'bakomai Alhaji,Allah ya raya mana abinda aka samu, kuma ai duk kokarin matarka tayi, don haka mu gode wa Allah gabaki ďaya' likita yace cikin nutsuwa,
'Zan iya shiga wurinsu yanzu likita', alhaji yace haďe da matsowa kusa da kofar dakin.
'nan da mintuna talatin nurses zasu gama shirya y'arka da matarka, in sun gama zasu sanar dakai' ,
'toh shikenan, godiya nake', murna yake sosai kamar an bashi kujerar makkah koda yaji likita ya ambato 'ya mace.
Ya ďađe yana adu'ar Allah ya bashi 'ya mace, saboda bai daďe da mahaifiyarshi ba kuma yana kudirin ya mata abubuwar alkhairi da yawa, tunda ayau bata nan, 'yarshi zaiyiwa.
Koda nurse ta kirashi, sai tunanin sa ya katse,
'yallabai, zaka iya ganinsu yanzu',
Bai iya amsata ba, yana sauri zai shi ga sai yaji kiran sunanshi daga nisa. Koda ya juya sai yaga makwabcinsa ne da ďan yaronsa wanda bai fiye shekara goma ba a tare dashi.
'A'a alhaji isa, lafiya kuwa, mai ya kawo ku asibiti ,ďan na tabbata bakasan da zuwan mu nan ba' ya karasa magana cikin mamaki,
'wallahi mun kawo farhan ne, bai jin ďaďi. Mun bar mamansa a can reception, zan kaisa a gwada jininsa ne',
'Allah sarki, toh Allah ya bashi lafiya. Nima na kawo uwar gidan ne, watan ta ya kai', ya ce yana murmushi.
'Ai bamu sani ba, me akasamu' alhaji isa ya tambayeshi cikin mamaki,
''ya mace aka samu, yanzu haka nima shiga zanyi in gansu',
' Ah, toh mu shiga tare', ya kama hannu farhan su ka shige ciki.
Farhan da tun da suka shigo baiyi magana, ya na hangan baby ya wuce wurinta ya tsaya yana kallonta shiru. Sai babansa ya maso kusa dashi ya ce,
'farhan, kaga sabuwar baby ko',
'eh dad, abamu mu tafi gida da ita', ya amsa cikin murya mai taushi.
Koda jin haka, sai alhaji sani ya kwashe da dariya, dama da shigowar su. Wajen matarsa ya nufa wanda ya samu tana bacci. Jin kalmar farhan yasa ya maso kusa dasu, yana faďin,
'farhan kenan, ai tayi karama da yawa. In mu ka baku yanzu, zatasha wahala. Amma zan iya bari ka rinka zuwa wurinta kullum ka ji ko? ',
Farhan ya gyada, amma kalmar data fito a bakinsa yasa kowa dariya har sai da matarsa sadiya ta farka.
'Toh dad, tazama my wife kenan', ya fađi tare da juyowa ya kalli babansa.
Wannan lokacin maman baby ce ta amsa mai,
'mai zai hana farhan, in lokaci yayi zamu baka ita'.
Hankalin kowa ya koma kanta, nan da nan aka fara gaisuwa. Alhaji sani ya maso gun matarsa yana bata magana, yana kuma sa mata albarka, gaskiya kowa yayi murna da wannan haihuwar.
Daga karshe alhaji isa da kyar yaja hannu farhan suka fita daga ďakin a yayin da yake cewa shi fa ya warke, kawai abarsa da matarsa wato sabuwar baby kenan.
Washe garin ranar, aka sallamesu daga asibiti bayan a tabbatar ba wani damuwa, sanan likita sukace a daure a rinka kawota allurar rigakafi. Koda suka dawo gida, ana ta shigowa daga makwabta gaisuwar samun karuwa. Saboda shi mai mutane ne, kowa sai da ji maganar haihuwar matarsa.
Alhaji sani dai, ďan kafanchan ne daga jahar kaduna. A angwan sakwatawa aka haifeshi, babansa nada mata biyu. A yayin da yafi kyautatawa wa ďaya yana barin ďaya, mamansa ce ake kuntatawa. Tunda ya tashi babansa bai ta'ba faranta masa ba, kullum cikin masifa na yau daban na gobe daban.
Sauran yan uwansa suna zuwa makaranta amma ba'asa shi ba, mahaifiyarshi tana iya kokarinta don taga ya samu ya tafi amma ina, dan sana'arta na kayan miya baya kawo kasuwa kuma mijinta baya taimaka mata. A lokaci shima yakan je aikin makanikanci, a hakan yasa kansa a makaranta har ya karasa primary. Kullum cikin wahala a gidan,gashi mahaifinshi baya tausaya masu hakan yasa mahaifiyarshi tasamu hawan jini wanda yayi ajalinta.

Uban gidanshi yana yawan faďa masa ya koma makaranta ta sakandari, saboda haka yasamu ya karasa har izuwa aji shida. Akwai wani alhaji dake zama a cikin garin kaduna, amma yana shigowa kafanchan yana ďan duba wasu kamfaninsa.
Yana kuma yawan kawo motarsa wurin aikinsu, koda yaga yadda yake da hankali sai yayi mai alkawarin in har zai biyoshi kaduna zai neman mai jami'a ta cikin gari a yayin da yake ta tayashi zama a wani shagonsa. Yayi murna sosai saboda yana son karatu kuma mahaifinshi baya kulashi gaba daya, shiyasa ya ga tunda ba wanda ke bukatarsa, ya shirya kayansa ya bi wannan alhajin kaduna.

Anan kaduna, ya karasa karatunsa har ya samu mata yayi aure. Alhaji ya neman masa aikin a wani banki tunda accounting ya karanta, gaskiya a rayuwa bazai ta'ba mantawa dashi.
Don haka kullum sai ya shiga ya gaisa dashi da tsafe kafin ya wuce wurin aiki, a haka har gashi Allah ya azurtashi da arzikin dashi da matarsa suka tafi aikin hajji suka dawo, sannan Allah ya albarkace shi da samun 'ya. Bai ta'ba zaton zai zamto haka ba, saboda wahalar daya sha a wurin mahaifinshi da kuma matar mahaifinshi.
Da mahaifiyarshi nada rai, daya biya mata duk wata bukatunta na duniya, bazata kuma ta'ba samun damuwa irin na hawan jini ba, Allah ya gafarta mata ameen.

Ranar suna
Anyi taro mai armashi, kowa yaci kuma yasha iya son ransa. Makwabta gaba ďaya an shigo kuma tasamu kyautuka sosai musaman daga wurin mijinta, saboda gani yake kaman an biya masa duk wasu bukatarsa da wannan 'yar.
Koda farhan suka shigo da mamansa, nacewa yayi sai an bar masa baby ya rike, da aka basa sai kuma yace baza a karbeta ba. Da kyar aka samu aka kwace a hannusa, wai shi sam da ita zai tafi gida.
Koda farhan suka shigo da mamansa, nacewa yayi sai an bar masa baby ya rike, da aka basa sai kuma yace baza a karbeta ba. Da kyar aka samu aka kwace a hannusa, wai shi sam da ita zai tafi gida.
Angama taron suna lafiya, yarinya tachi sunansa mahaifiyarshi, zainab wanda akewa lakabi da laila.
'Bangaren farhan
Tunda aka dawo gida, farhan ya 'bata rai kaman zaiyi kuka, mommysa tace,
'farhan, hope everything is well, duk ranka a 'bace tunda muka dawo',
Ya juya baya don kar ta ga fuskarsa sannan yace, 'gaskiya mommy i don't want to leave laila, a kawo mana ita mana',
Ta ďanyi murmushi, haďe da cewa 'farhan kenan, i can see that you are lonely koh, kana son kani ko kanwa '.
'A'a mommy i just want laila', ya faďi yayin da ya juyo yana nuna mata fuskarsa daya marairaice idanunsa,
'okay, naji bari dad ya dawo',
'toh, thank you mommy'.
Yana karasa faďin hakan, ya sake fuskarsa sannan ya wuce ďaki.
Shi dai alhaji isa haifefen garin kaduna ne, anan ya girma har ya karasa primary da sakandari dinsa. Iyayensa masu kudi ne sosai don haka baisha wahalar kammala karatunsa na jami'a ba wanda ya gama a ABU.
Koda ya gama sai suka turashi Australia saboda ya kammala masters dinsa gaba ďaya, anan ya hadu da matarsa hajiya hadiza wanda a lokacin degree dinta take karasawa. Sun shaku sosai, da dawowarsu aka hada masu aure tunda dama gidan kudi da kudi ne.
A hakan har Allah ya basu farhan, da mahaifinshi yayi niyar su wuce Sydney gaba daya amma alhaji isa yace sai farhan ya kara girma tukuna saboda ya gane kakanninsa kuma ya iya yaren hausa sosai koda yake yanzu dinma yakan hada hausan da turanci saboda hakan mamansa ta koya masa.

Da yamma, alhaji isa ya dawo matarsa ta bayyana mai yanda sukayi da farhan, ya kyalkyale da dariya sannan yace,
'farhan kenan akwai kuruciya, toh mu da muka kusan barin kasan nan, me na damuwa da farhan, by the time muna Sydney zai manta da ita',
'farhan kenan akwai kuruciya, toh mu da muka kusan barin kasan nan, me na damuwa da farhan, by the time muna Sydney zai manta da ita',
'Allah ya sa'.
Bayan sati ďaya
Alhaji isa suna ta shirye shiryen tafiya Sydney, farhan ko kullum sai ya ziyarci laila kuma kullum da kuka yake dawowa gida saboda baya son rabuwa da ita.
Koda yaji cewa zasuyi tafiya sai yayi tayin kuka wai saboda zai rabu da laila, amma dayaji Sydney zasu sai yayi murna sosai, sun ta'ba zuwa so ďaya lokacin da babansa ke duban gidan da zasu koma, kuma yaji daďin garin sosai.

Ranar da zasu tafi, da kyar aka sakashi a mota wai sai lallai su laila sun bisu, a haka sukayi sallama da kowa, anata faďin za'ayi kewarsu. A airport farhan ya daina kuka saboda yana bala'in son jirgi har cewa yake yanason zama pilot, babansa yace in Allah ya yarda you will be so my boy.
Sydney, Australia 🛥
Gari ne mai kyau gaske, ga ruwa ta ko ina ya zagaye shi. Sunada port wato inda jirgin ruwa ke aje kaya, ya kuma kwashesu, gari ne mai tarin tsuntsaye kalakala, gari mai ni'ima daku gidaje masu tarin armashi.
Kuma gashi sun sami gida a dai dai bakin ruwa, kunsan irin gidansu na turawa. The view is nice and wonderful, farhan ba karamin daďi yaji ba daya ga gidan, har ma ya manta maganan laila, sai salle yakeyi wai su mommy su fito su tafi bakin ruwa.
Bayan sun gama settling a gidan, sai alhaji isa ya fita don nemo wa farhan makaranta wanda suke kira da elementary 🏫 school ,sannan kuma ya leka firm dinsu na lauyoyi tunda shima babban lauya ne.
Bayan kwana biyu farhan da Iyayensa suka saba da zaman Sydney, weather ďin garin ya kar'be su sosai don duk sunyi kyau kuma sun kara haske kaman basu ba.

Bayan shekara goma
Ayau ake graduation ďin farhan na gama high school wato sakandari kenan, a kwana a tashi, da ikon Allah har ya gama. Gaba daya farhan ya canza, shekarunsa yanzu ashirin amma kamar yafi hakan. In ba hausa yayi ba, baza ka ta'ba cewa bahaushe bane, turanci ya zauna a bakinsa sosai.
Dama fari ne amma yanzu ya koma bature, ya kara tsayi da kuma kwarjini, ga hancin nan har baki, idanunsa dara dara gwanin kyau da saka zuciyar mai kallo bugawa, kana ganinsa kasan namiji ne da mata ke mutuwa masa, saboda faďaďďiyar kirjinsa, a irin shekarunsa kenan toh idan ya kai talatin fa ko fiye da hakan, gaskiya mata sai sun shiga uku.

Ga yanayin tafiyarsa ta katsaita kamar wani mai saurata, magana yakeyi da abokansa yana lumshe ido amma gaba ki ďaya matan wurin kallansa akeyi, dama shi ba kula su yakeyi ba. Sai dai kullum su rinka turo mai da love letter wato sakon soyayya amma bai ta'ba bada martani ba, gani yake ba macen da ta dauki hankalinsa a cikin su.
Kiran babansa yasa ya juya, a gefe guda ya hango mommy sa da dad. A guje ya wuce wurinsu ya hugging ďinsu duka,
'congratulations my son, gaskiya i can't tell you how happy I am today, me kakeso, ka faďamin, na maka alkawarin zan siya maka', babansa yace cike da farin ciki.
'Abu ďaya nake so dad', farhan ya amsa cikin natsuwa,
Mahaifinshi ya kalleshi shiru, bai ta'ba ganin ďa mai biyayya da rashin son abin duniya kaman ďanshi. Shiyasa yake matukar sonsa da kuma yabonsa, daga karshe dai yace,
'me kenan ďana',
Farhan yace 'dad, tunda nake karami nakeson zama pilot kuma har yanzu ban canza ba. So nake ka enrolling ďina a pilot institution ',
Alhaji isa ya ďanyi murmushi kaďan sannan yace 'na baka 100% yardana kuma naba dukkan support ďina, ka fara shirye shiryen tafiya sannan kuma zan saya maka Mercedes Benz of your choice saboda kamar wancan ta tsufa, sannan zan sa maka hajji na this year in kadawo kuma sai kafara school, kaji ko ďana.ko ya kace',
Farhan ya rasa abin cewa saboda haka ya rungume babansa yana kukan murna. Hajiya hadiza wanda tuntuni kallonsu takeyi sai tace,
' nikuma contributions ďina shine delicious food har sai kayi aure', gaba ďaya suka fashe da dariya, suka hugging juna gaba ďaya.
' nikuma contributions ďina shine delicious food har sai kayi aure', gaba ďaya suka fashe da dariya, suka hugging juna gaba ďaya.
Lots of 😍 love to you people, if not for you, i won't be here.
Nagode sosai, wannan shine sabon littafi na, wannan kuma shine first chapter, i hope you like it.
By voting i will know you love me so much, by commenting i will know how you feel about the book 🙂
Sai mun hadu a next chapter, thank you 😘😘😘
#Al-hubh❤❤❤

Comments